Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karon Battar Paris Saint Germain Da Manchester City, Karawa Ce Tsakanin Qatar Da Abu Dhabi


Karawar farko ta kwata fainal a gasar cin kofin zakarun kulob kulob na Turai, wadda za a yi yau laraba a tsakanin Paris Saint Germain ko PSG, da Manchester City, ba wai karawa ce a tsakanin kungiyoyin kwallon kafa biyu dake cikin wadanda suka fi arziki a nahiyar Turai ba, karawa ce ta kare mutunci a tsakanin wasu kasashen larabawa guda biyu, Abu Dhabi da Qatar.

Manchester City ta Ingila da PSG ta Faransa, biyu ne daga cikin kungiyoyin dake nuna yadda attajirai ‘yan kasashen waje suke mallake sha’anin kwallon kafar wasu kasashe a wannan zamanin.

Alkaluma sun nuna cewa wadannan kungiyoyin biyu, sun kashe tsabar kudi fiye da dala miliyan dubu 1 da dari 7 kan ‘yan wasa kawai.

Wannan karawar da za a yi ta janyo ra’ayin masoya tamaula a fadin yankin gabas ta tsakiya. Wani mai goyon bayan kwallon kafa na Qatar, Mohammed al-Jazali, yace lallai akwai gasa a tsakanin Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa a kan kowaccece take da kungiyar kwallo mafi karfi. Abu Dhabi dai tana daya daga cikin masarautu 7 da suka hadu suka yi Hadaddiyar Daular Larabawa.

Mutane a kafofin sada zumunta na intanet har sun sanya ma wannan karawar suna ko lakabi, wasu nace “El Cashico” watau kamar gasar masu kudi, da wadanda suke ce “Oil and Gasico” watau gasar masu mai da gas.

Masana tamaula sun ce ba don sa hannun attajirai daga kasashen yankin Gulf ba, zai yi wuya a yi wannan karawa a tsakanin kungiyoyin nan biyu, musamman ma a gasar cin kofin zakarun kulob kulob na Turai. A karkashin mallakar attajiran na yankin gulf, kungiyoyin biyu sun bunkasa suka shiga cikin jerin masu tasiri a duk fadin Turai, suka fara yin abubuwan da ba su taba yi ba a tarihinsu.

Alal ga misali, kafin wani kamfanin Qatar mai suna Qatar Sports Investment ya sayi kungiyar PSG ta Faransa a shekarar 2012, kungiyar sau biyu kawai ta taba lashe wasannin lig-lig na Faransa, kuma sau daya kawai ta ci wani kofi na UEFA.

Amma tun daga lokacin da ‘yan Qatar suka saye ta, ita ce take lashe gasar Lig a Faransa a jere, da kofin zakarun kulob na Faransa da kuma kofin kalubalenka na Faransa.

XS
SM
MD
LG