Buhari Ya Yi Alhanin Rasuwar John Chiahemen, Tsohon Shugaban Ofishin Kamfanin Dillancin Labarai Na Reuters

John Chiahemen

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa game da rasuwar John Chiahemen, tsohon shugaban ofishin kamfanin dillancin labarai na Reuters a Najeriya.

WASHINGTON, D.C - A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar, shugaba Buhari ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan Chiahemen, abokansa da abokan aikinsa, ciki har da kungiyoyin yada labarai daban-daban da ya yi aiki da su.

Shugaban ya tunatar da cewa, Chiahemen a matsayin tsohon dan jarida ta shaharar kamfanin dillancin labarai na kasa da kasa kuma Editan Reuters na Afrika, ya samu karbuwa saboda irin gudummawar da ya bayar da kuma matsayinsa na edita na yada labarai game da Afirka ta fuskar kasuwanci da ci gaba.

Ya yi addu’ar Allah ya jikan marigayin ya kuma baiwa wadanda suka yi alhinin fitawarsa ta’aziyya.

Chiahemen ya kuma yi aiki da kamfanin yada labarai na Abubakar Atiku Gotel a matsayin manajan darakta na farko a shekarar 2015.