Buhari Ya Tafi Kasar Habasha 

Lokacin da shugaba Buhari ya kama hanyarsa ta zuwa London (Facebook/Femi Adesina)

Ziyarar ta Buhari a Ethiopia na zuwa ne mako guda bayan da ya dawo daga Amurka inda ya halarci taron Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a birnin New York.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tafi kasar Habasha don halartar bikin rantsar da Firai Minista Abiy Ahmed a sabon wa’adi na biyu da za a yi a ranar Litinin.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar a ranar Asabar ta ce, shugaba Buhari na daga cikin manyan bakin da za su yi jawabi a bikin rantsar da Ahmed.

Daga cikin wadanda suka rufa masa baya a cewar sanarwar wacce Kakakinsa Femi Adesina ya fitar, akwai “Ministan harkokin wajen Geoffrey Onyeama da Babban Darektan hukumar tattara bayanan sirri Ambasada Ahmed Rufai Abubakar.”

“A ranar Talata ake sa ran zai dawo Abuja,” Adesina ya kara da cewa.

A ranar Lahadi Buhari ya dawo daga taron Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a karo na 76 a Amurka bayan kwashe mako guda a can.

Firai Ministan Ahmed ya samu nasarar wani sabon wa’adin shekara biyar ne bayan da jam’iyyarsa ta Prosperity Party mai mulki ta samu nasara a zaben ‘yan majalisar da aka yi a ranar 21 ga watan Yuni.

Tun bayan samun nasarar shugaban Najeriya ya taya Ahmed murnar lashe zaben inda ya tabbatarwa da kasar cewa “Najeriya za ta ci gaba da tallafa mata da sauren kasashen nahiyar wajen hadin kasa da zaman lafiya a yankunansu.