Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Zai Tafi Kasar Habasha


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce a ranar Talata Buhari zai dawo Abuja.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyara kasar Habasha don halartar bikin rantsar da Firai Minista Abiy Ahmed a sabon wa’adi na biyu da za a yi a ranar Litinin.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar a ranar Asabar ta ce, a ranar Lahadi Buhari zai kama hanyarsa ta zuwa kasar ta Ethiopia inda zai yi jawabi a taron rantsar da Ahmed.

Daga cikin wadanda za su rufa masa baya a cewar sanarwar wacce Kakakinsa Femi Adesina ya fitar, akwai “Ministan harkokin wajen Geoffrey Onyeama da Babban Darektan hukumar tattara bayanan sirri Ambasada Ahmed Rufai Abubakar.”

“A ranar Talata ake sa ran zai dawo Abuja,” Adesina ya kara da cewa.

A ranar Lahadi Buhari ya dawo daga taron Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a karo na 76 a Amurka bayan kwashe mako guda a can.

Firai Ministan Ahmed ya samu nasarar wani sabon wa’adin shekara biyar ne bayan da jam’iyyarsa ta Prosperity Party mai mulki ta samu nasara a zaben ‘yan majalisar da aka yi a ranar 21 ga watan Yuni.

Tun bayan samun nasarar shugaban Najeriya ya taya Ahmed murnar lashe zaben inda ya tabbatarwa da kasar cewa “Najeriya za ta ci gaba da tallafa mata da sauren kasashen nahiyar wajen hadin kasa da zaman lafiya a yankunansu.

XS
SM
MD
LG