Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Isa Paris, Zai Gana Da Macron Kan Matsalar Tsaro


Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, a lokacin da ya isa birnin Paris (Twitter/ @BashirAhmaad)
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, a lokacin da ya isa birnin Paris (Twitter/ @BashirAhmaad)

Taron, wanda Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai jagoranta, har ila yau zai duba yadda za a saukakawa kasashen nahiyar basukan da ake bin su.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tafi birnin Paris da ke Faransa, don halartar wani taron koli, wanda zai mayar da hankali kan duba irin tasirin da annobar coronavirus ta yi akan tattalin arzikin nahiyar Afirka.

Buhari zai kwashe kwana hudu a wannan ziyara.

Taron wanda Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai jagoranta na duba yadda za a saukakawa kasashen nahiyar basukan da ake bin su.

“Shugaba Buhari zai bar Abuja don zuwa birnin Paris na kasar Faransa a ranar Lahadi 16 ga watan Mayu.” Wata sanarwa da Kakakin Buhari, Garba Shehu ya fada a wara sanarwa gabanin tafiyar shugaban.

Karin bayani akan: ​Emmanuel Macron, Faransa, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

“A lokacin wannan ziyarar, Shugaba Muhammadu Buhari, zai hadu da takwaran aikinsa Emmanuel Macron, inda za su tattauna kan karuwar matsalolin tsaro a yankin Sahel da kuma Tafkin Chadi.” In ji Shehu.

Shugaba Buhari da jami'an gwamnatinsa da suka masa rakiya a masaukinsu na Paris (Twitter/ @BashirAhmaad)
Shugaba Buhari da jami'an gwamnatinsa da suka masa rakiya a masaukinsu na Paris (Twitter/ @BashirAhmaad)

Hakazalika, Buhari zai tattauna da Shugaba Emmanuel Macron kan batutuwan da suka shafi siyasar kasashen biyu, tattalin arziki, sauyin yanayi da kuma yadda za su kulla alaka a fannin kiwon lafiya.

“Musamman kan abin da ya shafi fannin yaduwar cutar COVID-19 da bincike da kuma samar da allurar riga-kafinta.”

Shugaban Najeriya a cewar sanarwar, zai kuma gana da wasu rukunin masu harkar mai da gas, kwararru a fannin sadarwa da kuma ‘yan Najeriya mazauna kasar Faransa.

Buhari zai samu rakiyar Ministan harkokin kasashen ketare, Geoffery Onyeama, Ministar kudi da tsare kasafin kudi, Zainab Shamsuna Ahmed, Ministan kasuwanci da saka hannayen jari, Otumba Adeniyi da kuma Ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire.

A ranar 30 ga watan Maris shugaban na Najeriya ya tafi London don duba lafiyarsa inda ya kwashe makonni biyu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG