Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dage ziyarar da zai kai birnin London na Birtaniya don duba lafiyarsa.
Wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar a ranar Juma'a ce ta bayyana hakan.
Sai dai fadar shugaban kasar ba ta bayyana dalilin dage tafiyar ba.
"Za a bayyana ranar da zai yi tafiyar a nan gaba." In ji Adesina.
A ranar Alhamis fadar shugaban kasar ta sanar da cewa Buharin zai tafi London a ranar Juma’a don sake ganin likita.
“Buhari zai tafi birnin London na kasar Birtaniya a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuni 2021, don komawa ya sake bibiyar lafiyarsa.” Wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar ta ce.
Karin bayani akan: London, Birtaniya, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
A baya an tsara akan cewa shugaban zai dawo a mako na biyu cikin watan Yulin da ke tafe a cewar Adesina.
A watan Maris Buhari ya je kasar ta Birtaniya inda ya je duba lafiyarsa, ya kuma kwashe kusan mako biyu a can kafin ya koma gida.
Da tafiyar ta yi wu, da ta kasance ziyara ta biyu cikin kasa da wata uku da shugaban zai kai London don ganin likita.
A shekarun baya, shugaban na Najeriya ya kan je a duba lafiyarsa, illa a bara da bai je ba, saboda annobar COVID-19 da ta karade duniya, ta kuma sa aka rufe hanyoyin tafiye-tafiye.