Baya ga Dasuki, har ila yau shugaban ya ba da umurni a tsare wasu mutane da ke da hanu a wannan badakala bayan bincike da aka gudanar na fannin tsaro tun daga yanzu 2007 zuwa.
A watan Agusta aka kafa wani kwamiti mai dauke da mutane 13 domin gudanar da cikakken bincike kan yadda aka tafiyar da kudaden sayen makamai.
Shugaba Buhari ya ba da umurnin a tsare Dasuki ne bayan da kwamitin ya gabatar da rahotonsa na wucin gadi, kamar yadda wata sanarwar da babban mai baiwa shugaban shawara, Femi Adesina ta nuna.
Ana dai zargin wadanda aka tsare ne da karkata akalar kudaden da yawansu ya kai sama da dala biliyan biyu baya ga wasu miliyoyin nairori.
Dama dai Dasuki na karakashin daurin talalala ne a gidansa da ke Abuja inda yanzu haka lamarin ke kotu bayan da ya shigar da bukatar yana so ya je kasar waje neman magani.
Dasuki shi ne ya kasance mai baiwa tsohon shugaban kasar shawara, wato Dr Goodluck Jonathan wanda Buhari ya doke a zaben da ya gabata.
Saurari rahoton Nasiru Adamu Elhikaya domin jin karin bayani:
Your browser doesn’t support HTML5