Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Zai Yi Adalci Ma Mata, Inji Hafsat Baba


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Yayin da ake ta korafe-korafen cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba ta tafi da mata yadda ya kamata ba, wata fitacciyar 'yar rajin muradun mata ta ce lokaci bai yi na zargin gwamnatin Buhari da kin tafiya da mata ba.

Wata fitacciyar ‘yar siyasa da ke zaune a birnin Kadunan arewacin Najeriya mai suna Hafsat Baba ta yi kira ga ‘yan’uwanta mata da su yi hakuri game da batun raba mukami a gwamnatin Najeriya tunda, a cewarta, yanzu aka fara.

A hira da abokin aikinmu Usman Kabara, Hajiya Hafsat ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ya sha jaddada cewa zai tafi da mata a gwamnatinsa, ba zai yi watsi da sub a. Ta ce ko Ministar Mata, Hajiya Jummai Alhassan kasancewarta Sanata, ta san al’amuran da su ka shafi mata sosai. Kodayake ta na fatan za ta dare kan kujerar gwamnan jahar Taraba kamar yadda alamu ke nunawa, inji Hajiya Hafsat.

Hajiya Hafsat ta ce ba wai mata na neman daidaita kansu da mata ba ne. So kawai su ke ayi dalci. Kuma bai kamata a rinka ruruta laifin mata ana sakaya na maza ba.

Ga cikakkiyar hirar:

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:14 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG