Britaniya Har Yanzu Akwai Sauran Rina A Kaba

Firayim Minister Theresa May

Har yanzu Theresa May na neman jama'iyyar da zata mara mata baya domin ta sami kafa Gwamnati

Har yanzu firayim minister Britaniya ‘yar jam’iyyar Conservative ta masu ra’ayin rikau tana kokarin cimma yarjejeniyar da zata ba ta goyon bayan da take bukata domin kafa gwamnati tare da jam’iyyar Democratic Unionist ta Yankin Ireland ta Arewa.

Wata sanarwar da aka samu yau lahadi daga ofishin Theresa May ta ce a bisa dukkan alamu cikin wannan sabon satin da aka shiga za a kamala wannan yarjejeniya ta goyon baya. Irin wannan yarjejeniyar goyon baya ba ta da karfi kamar cikakkiyar yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin kai ko kawance a tsakanin jam’iyyun. Abinda kawai take nufi shine jam’iyyar DUP zata goyi bayan gwamnati a duk wani batu na kasafin kudi ko kuma idan an zo jefa kuri’ar amincewa ko kin amincewa da gwamnati. Amma duk sauran batutuwan, jam’iyyar DUP tana iya rungumar matsayin da ya saba da na ‘yan Conservative.

Wata sanarwar da jam’iyyar DUP ta bayar ta ce ya zuwa yanzu dai tattaunawar tasu tana yin tasiri.

May tana bukatar goyon bayan wakilai akalla 326 a majalisar dokoki domin ta kafa gwamnati. ‘Yan Conservative sun samu kujeru 318 a zaben da aka yi, yayin da DUP ta lashe kujeru 10.

Ana bukatar sassan biyu su cimma yarjejeniya kafin ranar 19 ga watan nan na Yuni, lokacin da Sarauniya Elizabeth zata gabatar da jawabin ayyana shirye-shiryen gwamnati.