Hukumomin kasar Iran sunce Amurka da Saudi Arabia ne suke dorawa laifin bada goyon baya ga mutanen da suka kai hari a majalisar dokoki da wata muhimmiyar makabarta dake birnin Tehran inda aka kashe mutane 17.
A lokacin da yake jawabi wajen jana’izar da dubban mutane suka halarta,shugaban addini na Iran din, Ayatollah Ali Khamenei yace wannan harin da aka kai ranar Larabar da ta gabata ba abinda zaiyi illa sa mutanen Iran su kara tsanantar gwamnatocin America da na Sa’udiyyar.
Ayatollah din yace tagwayen hare-haren da aka kai a kan majalisar dokokin da kuma kan makabartar tsohon shugaban addinin Iran Ayatollah Ruhollah Khomeini ba zasu “sa gwiwar mutanen Iran tayi rauni ba” ko kadan.
Duk da cewa tuni kungiyar ISIS ta dauki alkhakin kai hare-haren biyu, dubban mutanen da suka halarci jana’izar mamatan sunyi ta ihun la’antar Amurka da kira akan a hallaka dukkan ‘yan gidan sarautar Saudi Arabia din.
A halin yanzu kuma hukumomin Iran din sun kame mutane akalla 41 da ake jin suna da hannu a cikin farmakin a wasu samame da ma’aikatan tsaro suka kai a nan cikin Teheran da kuma wasu sassa na lardunan Kurdawa dake yammacin kasar.
Facebook Forum