Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Trump Ya Dauka Shaidar Comey Ta Wankeshi


Shugaba Trump da Comey tsohon shugaban FBI wanda Trump ya tsige
Shugaba Trump da Comey tsohon shugaban FBI wanda Trump ya tsige

Shugaban Amurka Donald Trump ya dauki shaidar da tsohon shugaban hukumar FBI ya bayar jiya wa kwamitin tsaro na majalisar dattijai kan kutsen Rasha a harkokin zaben bara tamkar an wankeshi ne

Bayan shiru na ba-sabam ba da yayi jiya Alhamis a shafinsa na Twitter, ranar da tsohon darektan hukumar binciken manyan laifuffuka ta FBI James Comey, ya fadawa ‘yan majalisa cewa ba shugaba Donald Trump ake hari ba a binciken katsalandar Rasha a zaben Amurka, shugaban na Amurka ya bayyana a shafin nasa yau Jumma’a yana cewa an wanke shi, yayin da yake bayyana Comey a zaman mai kwarmato.

Trump ya kori Comey a watan Mayu inda yace “Al’amarin Rasha” yana ransa a lokacin da ya kori shugaban babbar hukumar binciken ta kasa a lokacin da yake jagorancin binciken da hukumar ta FBI take yi kan irin kutsen da Rasha ta yi a harkokin zaben Amurka a shekarar da ta shige.

Comey dai ya gabatar da shaida jiya Alhamis a gaban kwamitin kula da ayyukan leken asiri na majalisar dattijai, inda ya ce yayi imanin Trump yana kokarin sanya shi ya watsar da binciken da suke yi ne na tsohon mai ba shugaban shawara kan harkokin tsaron kasa, haka kuma jami’an fadar White House sun yada karairayi domin boye dalilin zahiri na korarsa.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG