Rundunar Sojan ta fitar da wani sanarwa cewa ta gano ta kuma lalata masana’antun hada boma bomai a jahar Borno
WASHINGTON, DC —
An samu tashin Boma-Bomai a garin Damaturu, a lokacin da jama’a ke hada hada, wanda ake zargin cewa wasu ‘yan kunar bakin wake ne suka kai wannan harin da yayi sanadiyar mutuwar muane 16.
Tashin Boma-Bomai dai yazo ne dai dai lokacin da rundunar Sojan ke fitar da wani sanarwa cewa ta gano ta kuma lalata masana’antun hada boma bomai a jahar Borno, wanda mataimakin darakta mai hulda da jama’a na rundunar Sojan Kanar Sani Usman Kuka Sheka, ya aikewa manema labarai.
Alhaji Musa Idi Dijawa babban sakatare a hukumar samarda agajin gaggawa na jahar Yobe ya tabbatar wa muryar Amurka afkuwar lamarin.
Ya kuma kara da cewa wadanda suka ji rauni kuwa suna asibiti suna karban magani.
Your browser doesn’t support HTML5