Jiya Litinin, Amurka da wasu kasshen dake yankin Pacific suka cimma yarjejeniya kan batutwa masu yawa da zasu rage haraji da kawar da shingayen cinikayya, da zai shafi kusan rabin tattalin arzikin duniya.
Yarjejeniyar da ake kira Trans-Pacific Partnership ko TPP a takaice, gagarumar nasara ce a fannin manufofin harkokin kasshen waje ga shugaba Barack Obama, koda shike babu tabbas ko majalisar dokokin Amurka zata amince da ita. Shugaban yace, "yarjejeniyar ta nuna irin abubuwa da Amurkawa suka yi amanna dasu, kuma daidaiton zai baiwa ma'aikata a nan Amurka damar samun ci gaban da cancanci samu".
Mr. Obama yace, Amurka ba zata kyale kasashe irinsu China su rubuta ka'idodjin cinikayya ga tattalin arzikin duniya ba. Yace tilas ne su rubuta wadannan dokoki, tareda kafa mizani mai karfi na kare ma'aikata da mutunta muhalli".
Masu fashin baki sun ce wannan yarjejeniya zata iya takawa bunkasar da China take yi birki, kasar da yanzu tattalin arzikinta shine na biyu a girma a duniya.
An dauki shekaru bakwai ana gudanar da shawarwari, a wasu lokuta zazzafawar muhawara kamin a kammala. Har yanzu ma da sauran bayanai da za'a fitar nan gaba.