Jahar Adamawa, tare da taimakon hukumar Asusun Tallafa wa Yara (UINCEF,) ta kaddamar da shirin sake maida yara dubu 56 makaranta, musamman a kananan hukumomi bakwai da a baya ‘yan Boko Haram su ka addaba.
Wakilinmu a shiyyar Adamawa wanda ya aiko da labarin, Ibrahim Abdul’aziz, ya ce ‘yan Boko Haram sun yi illa sosai ga yankuna masu yawa ciki har da kashe malamai da ‘yan makaranta, tare kuma da hana yara cigaba da karatunsu. Ibrahim ya je sansanin ‘yan gudun hijira na Malkwai, inda ya tarar da yara na karatu a wani yanayi.
Da ta ke kaddamar da wani bangare na shirin na maido da ‘yan makarantan a Karamar Hukumar Maiha, Kwamishiniyar Harkokin Ilimi a Jahar Adamawa Dr. Kaleptawa Farauta ta ce ana daukar wannan matakin ne saboda babu wani zabin da ya fi. Ta ce idan ba a sake maida yaran a makarantu ba, sun a iya fadawa hannun miyagu ciki har da ‘yan Boko Haram.
Shi ma da yak e jawabi, Jami’in Asusun Tallafa Ma Yaran a Shiyyar Bauchi, Dr Abdullahi Kaikai y ace Asusun zai tashi haikan wajen maido da yaran makaranta baya ga wasu matakan da za ta dauka na inganta ilimi da makomar yaran. Su ma yaran sun nuna farin cikinsu game da wannan matakin.