Yau ne Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Abubakar Bukola Saraki ya karanta sunayen Ministocin da Shugaba Muhammadu Buhari ya mika ma Majalisar don tantancewa. Wakiliyarmu a Abuja Madina Dauda ta ruwaito Shugaban Majalisar Dattawan na cewa karanta sunayen Ministocin, wadanda su ka hada da: Abubakar Malami, daga jahar Kebbi; da Janar Abdurrahman Bello Danbazau daga jahar Kano; da Aisha Jummai Alhassan, daga jahar Taraba; da Alhaji Laye Muhammed; da Babatunde Raji Fashola daga jahar Lagos; da Barrister Adebayo Shittu; da Barrister Solomon Dalong, daga jahar Filato.
Sauran mutanen da aka gabatar da sunayensu don tantancewar sun hada da Sanata Chris Ngige daga jahar Anambra; da Rotimi Amaechi, jahar Rivers; da Chief Audu Innocent Ogbeh, daga jahar Kogi; da Mrs Amina Ibrahim; da Dr. Osage ENARE da Dr Emanuel Ebe Kachukwu da Dr Kayode Fayemi , jahar Ekoiti; da Injiniya Suleiman Adamu da Mrs Kemi Adiosun; da Dr. Ogbunaya Onu, jahar Abia; da Ahmed Isa Ibeto, daga jahar Nasarawa; da Ibrahim Usman Jibrin da Sanata Hadi Sirika, daga jahar Katsina; da Sanata Udoma Udo Udoma, daga jahar Akwa-Ibom.
Tuni dai aka fara cece-kuce kan sunayen. Wani Sanata dan jam’iyyar PDP y ace da sun yi tsammanin za a gabatar da sunayen wasu sabbin mutane ne, to amma sai gashi mutanen da su ka sani ne. Hasalima, in ji shi, wasunsu sun yi aiki tare. Y ace duk da haka za su gayyaci hukumomin ICPC da EFCC su binciki kowannensu.
Shi kuwa wani dan jam’iyyar APC Sanata Mohammed Shaba Lafiagi y ace za a bi tsarin da aka saba bi ne wajen tantancewar.
Madina ta ce ranar Talata mai zuwa 13 ga wata ne za a yi tantancewar.