Wasu da ake zargin ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram sun yi yunkurin kai wani hari a yammacin ranar Lahadi da ta gabata, wanda rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar dakile shi.
Wasu mazauna garin Damaturu na jahar Yobe da ke arewa maso gabashin kasar sun shaidawa Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa suna ta jin karar shawagin jiragen yakin sojan kasar da kuma karar manyan bidigogi anata harbe harbe.
Sannan mazauna garin sun yi kira ga gwamnati da ta rinka daukan matakai akan wadannan miyagu kafin su kawo hari a cikin garuruwan su.
Wata majiya mai tushe daga rundunar sojan Najeriya ta tabbatarwa Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun yi yunkurin kai hari, amma rundunar sojan ta dakile shi.
Wani masanin tsaro ya ce a jihar Yobe ne wannan ta’addanci na kungiyar Boko Haram ya fara kafin ya bazu zuwa jihar Borno, wanda ya watsu zuwa wasu sauran garuruwa.
Ya kuma bukaci dakarun tsaron Najeriya da su nunawa duniya cewa suna aiki tukuru wajan magance wannan matsalar data ki ci taki cinyewa.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina:
Your browser doesn’t support HTML5