Wannan gyara dai zai faru ne domin an samu kari akan kasafin na Naira Triliyan 10 da digo 3, da ya mika wa hadaddiyar Majalisa a watan Oktoba na bana.
Kasafin na shekara 2020 ya karu ne da Naira Biliyan dari biyu da sittin da hudu { 264 Billion Naira} kuma hakan ya faru ne a sakamakon karin da Majalisar kasa ta yi akan kudin gangan danyen man fetur daga dalar Amurka 55 da shugaban kasa ya kawo zuwa dalar Amurka 57, wani abu da shugaban kwamitin kula da aiyukan na musamman Sanata Yusuf Abubakar Yusuf ya ce sai da Majalisa ta tuntubi ma'aikatar man fetur da OPEC akan sauyi da ake samu a kasuwar duniya kafin su daga kudin da karin dalar Amurka 2 kacal, kuma wanan jimlar ita ce ta kara kasafin daga Naira Triliyan 10.330 zuwa Naira Triliyan 10.594.
Wannan yana iya faruwa a duk lokacin da aka samu karin kudi irin wannan wanda zai sa shugaban kasa ya nemi izinin kashe kudin daga wurin Majalisar Dokokin kasa, duk da cewa ya riga ya sa hannu a kasafin kudin wanda ake kira VIREMENT a harshen turanci kamar yadda kwararre a fanin tattalin arzikin kasa da kasa Yusha'u Aliyu ya ce dole ne a bi wanan ka'ida kafin a kashe kasafin, saboda karin da aka samu bayan an kaiga sa hannu kasafin ya zama doka.
Majalisar Dokokin Najeriya ta fara hutun ta na karshen shekara wanda zai kai ranar 28 ga watan Janirun shekara 2020 kafin su dawo bakin aiki.
Ga karin bayani a sauti:
Facebook Forum