Boko Haram Na Kwararawa Zuwa Bauchi Daga Yobe - Gwamnati

  • Murtala Sanyinna

Boko Haram

Gwamnatin jihar Bauchi ta ankarar da jama’ar jihar cewa ana zargin ‘yan kungiyar Boko Haram suna kwararowa daga Geidam ta jihar Yobe zuwa cikin jihar.

A yayin wata ganawa da manema labarai bayan kammala wani taron gaggawa akan sha’anin tsaro, sakataren gwamnatin jihar ta Bauchi Alhaji Sabiu Baba, ya ce an lura da kwararowar wasu bakin fuskoki a yankunan kananan hukumomin jihar.

Baba ya ce abin da ya faru a Geidam, ya yi sanadiyyar shigowar jama’a da dama daga jihar Yobe, domin kuwa jihar ta Bauchi tana makwabtaka da Yobe a kananan hukumomi 4 na Zaki, Dambam, Darazo da Gamawa.

Gov Bala Muh'd

Karin bayani akan: Boko Haram​, Nigeria, da Najeriya.

Ko baya ga barazana a sha’anin tsaro sakamakon shigowar ‘yan kungiyar ta Boko Haram, sakataren gwamnatin yace kwararowar ‘yan gudun hijira daga jihar Yobe sakamakon hare-haren kungiyar, shi ma kan iya haifar da wani kalubale ga tattalin arzikin jihar ta Bauchi.

To sai dai ya ce gwamnati tana tattaunawa da hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki a sha’anin tsaro, domin samar da maslaha da dakile ayukan ta’addaci kafin su yadu a jihar.