Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Najeriya Ta Nesanta Kanta Daga Batun Karbar Mulkin Kasar


Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Ranar Soja A Zamfara
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:19 0:00

Shugaba Muhammadu Buhari cikin kayan Soja tare da ministan tsaro Janar Mansur Dan Ali mai ritaya da sauran jami'an hafsoshin sojan Najeriya wajen kaddamar da Ranar Sojoji Ta Kasa a garin Dansadau a Jihar Zamfara.

Rundunar sojin Najeriya ta maida martani akan kiraye-kirayen da ake yi na cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari ya mika mata mulkin kasar domin ceto ta daga wargajewa.

Wani babban lauya a kasar Robert Clarke ne, ya shawarci shugaba Muhammadu Buhari da ya mika mulki na dan lokaci ga rundunar sojin kasar, domin ta samar da maslaha akan dimbin matsalolin tsaro da tattalin arziki da suka yi wa kasar katutu.

A yayin da yake tsokaci a gidan talabijin na CHANNELS, Clarke ya ce sha’anin tabarbarewar tsaro ya kai halin la haula a kasar, ta yadda “soja ne kadai za su iya magance wadannan matsalolin a halin yanzu.”

Clarke, wanda ya ce Najeriya ta kama turbar wargajewa sakamakon rashin tsaro, ya bayyana cewa kamata yayi soji su karbi iko na wuccin gadi, su kuma mayar da kasar bisa tsarin jihohi 6 kamar yadda ta taba zama a can baya.

Babban Lauya Robert Clarke
Babban Lauya Robert Clarke

A cewar babban lauyan, shugaba Muhammadu Buhari na da karfin iko a karkashin kundin tsarin mulki na 1999, da zai mika mulki na dan lokaci ga rundunar soji, tare da dora mata nauyin mayar da kasar a tsarin na jihohi 6 domin daidaita al’amura.

“Kasar nan na bukatar dokar ta baci. Kamata yayi shugaba Buhari ya tattauna da ‘yan majalisun dokoki na tarayya da na jihohi da kuma gwamnoni akan saka dokar nan take,” in ji lauya Clarke.

Karin bayani akan: Boko Haram, CHANNELS, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

To sai dai da take maida martani akan wannan batu, rundunar sojin kasar ta ce za ta ci gaba da tsayuwa kaimun kan biyayya ga gwamnati mai ci yanzu, da kuma dukkan tanade-tanaden mulkin dimokaradiyya.

A wata sanarwa daga Daraktan watsa labarai na rundunar tsaro, Janar Onyema Nwachukwu, ta ce rundunar “za ta ci gaba da kauracewa siyasa, goyon bayan gwamnatin farar hula, da kuma da’a da biyayya ga shugaban kasa da kuma kundin tsarin mulkin kasa.”

Shugaban Najeria Muhammadu buhari Tare da manyan hafsoshin tsaro
Shugaban Najeria Muhammadu buhari Tare da manyan hafsoshin tsaro

Nwachukwu ya kara da cewa sojin kasar za su ci gaba da aiwatar da ayukansu bisa kwarewa, na kare martabar dimokaradiyya da mutuncin kasa, kazalika da kuma tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.

Don haka sanarwar ta gargadi ‘yan siyasa da ke ruruta wutar rikicin neman hambarar da gwamnati ta haramtacciyar hanya da su shiga taitayinsu, domin kuwa rundunar sojin a tsaye take wajen kare dimokaradiyya.

Ta kuma tunatar da dukkan jami’an sojin kasar cewa babban laifi ne su ma yi tunanin tsunduma a wannan keta dokar, inda kuma ta sha alwashin hukunta duk wani jami’in soji da ya yarda ya karbi hudubar irin wadannan ‘yan siyasar.

Buhari Ya Jagoranci Taron Tsaron Kasa Tare Da Manyan Shugabannin Hukumomin Tsaron Najeriya
Buhari Ya Jagoranci Taron Tsaron Kasa Tare Da Manyan Shugabannin Hukumomin Tsaron Najeriya

Duk da yake sanarwar ta tabbatar da cewa kasar na cikin wani mawuyacin hali, to amma ta ce tana hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin samo bakin zaren warware matsalolin, tare da baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewa “al’amura za su daidaita nan ba da jimawa ba.

A baya-bayan nan dai, Najeriya ta rasa sojoji da dama a yayin da suke aikin tsaron kasa sakamakon hare-haren mayakan Boko Haram a yankunan arewa maso gaba musamman jihohin Borno da Yobe.

Haka ma wani shugaban dakarun sojojin kasar da wasu manyan jami’ai bakwai sun mutu a lokacin da ‘yan Boko Haram suka kai wani hari a jihar Borno a baya-bayan nan.

Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji
Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji

Najeriya dai na fama da matsalolin tsaro a kusan dukannin yankunan ta kama da mayakan Boko Haram a yankunan arewa maso gabas, ‘yan bindiga dadi da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa a arewa maso yamma, ayyukan tada zaune tsaye na haramtaccen kungiyar IPOB, mai fafutukar kafa kasar Biyafara, a kudancin kasar, da dai sauran su.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG