Rahotanni daga Najeriya na cewa wani jirgin yakin saman Najeriya ya kashe wasu dakarun kasar bisa kuskure a yankin Mainok na jihar Borno da ke arewacin kasar.
Dakarun saman na taimakawa takwarorin aikinsu na kasa ne a yakin da Najeriya ke yi da mayakan Boko Haram da na ISWAP.
Wasu rahotanni sun ce adadin sojojin da aka kashe a wannan hari ya kai 30.
Karin bayani akan: ISWAP, jihar Borno, Boko Haram, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Sai dai rundunar sojin saman Najeriyar, ta fitar da wata sanarwa a ranar Litinin a shafinta na Twitter.
Ta ce ita ma ta ga rahotannin da wani bidiyo da yake ta yawo a shafukan sada zumunta da ke nuna harin da aka kai bisa kuskure, inda ta ce, tana kan bincike kan sahihancinsa.
“An ja hankalin rundunar sojin Najeriya, inda rahotanni ke cewa “yadda rundunar sojin saman Najeriya ta kashe sojoji 20 bisa kuskure a wani harin sama” a Mainok da ke da tazarar tafiyar kilomita 55 daga Maidguri.” Sanarwar ta Twitter ta ce.
Ta kara da cewa, “rundunar sojin saman Najeriya (NAF) na gudanar da bincike kan hoton bidiyo da rahotanni da ke ta yawo, kuma za a sanar da jama’a sakamakon binciken da zarar an kammala.”
A watan Janairun shekarar 2017, wani jirgin yakin sama na Najeriya ya kashe fararen hula sama da 100 a garin Rann da ke jihar Borno.
Lamarin ya faru ne bayan da jirgin yakin ya saki bama-bamai akan wani sansanin ‘yan gudun hijira bisa kuskure.
A ‘yan kwanakin nan, mayakan ISWAP da Boko Haram, sun yi ta kai hari a yankunan jihar Borno da Yobe.
Hakan ya sa jama’a da dama tserewa daga yankunan domin tsira da rayukansu.
Wasu rahotannin sun ce garin Geidam yanzu haka yana hannun kungiyar Boko Haram.
Yayin wani taron manema labarai da ya yi, Gwamnan Yobe Mai Mala Buni, ya bayyana irin mawuyacin halin da mayakan suka jefa garin na Geidam da suke ta kai wa hari tun daga ranar Juma’a.