Kakakin rundunar Kanar Timothy Antiga ya shaidawa muryar Amurka cewa, bayanan sirri da aka tattaro sun tabbatar da hakan, yayinda wadansu mazauna yankin da kungiyoyi suka jadada hakan.
Kanar Antiga yace suma kansu sojojin sun tabbatar da haka yayin da suka wallafa hotunan wasu yara kanana da aka sanya su cikin aikin sojin dauke da manyan bindigogi.
Rundunar a yankin tafkin chadin tace wannan faruwa ne bayan da a baya kungiyar boko haram tayi ta sace yan mata dalibai, tana cin zarafin mata da ma kashe mutane fararar hula da basu ji ba basu gani ba.
Rundunar dakarun tafkin chadin tace sanya kananan yara aikin soji na zuwa ne ganin yanzu dakaru sun wargaza yan Boko Haram din a yankin al'amarin da ya sa da dama daga cikin mayakanta suka mika wuya ga dakarun MNJTF.
Sojojin yankin tafkin chadin suka ce sanya yara aikin soja ya sabawa yarjejeniyar majalisar dinkin duniya kan kare kananan yara, don haka sun nemi majalisar tayi Allah wadai da hakan , kana tace a nata bangaren zata matsa kaimi wajen kawo karshen yan ta'addan.
Tuni dai masu rajin kare hakkin yara suke nuna rashin jin dadi bisa irin wannan sabon salo na yan ta'addan.
Saurari rahoton Hassan Maina Kaina cikin sauti
Your browser doesn’t support HTML5