Dakarun yankin tafkin Chadi tare da hadin gwiwar abokan kawancensu da kuma Jiragen yakin rundunar Operation Lafiya Dole da na sojojin saman kasar Nijer sun yi dirar mikiya akan wani sansanin mayakan ISWAP inda suka rugurguza shi.
A wata sanarwar da ya tura wa Muryar Amurka, kakakin rundunar Kanal Timothy Antiga, ya tabbatar da cewa sojojin sun kai farmakin da ya yi sanadiyyar kashe manyan mayakan ISWAP guda arba'in da takwas.
Wani bayanin sirri da Shelkwatar rundunar dakarun tafkin Chadi ta samu akan inda mayakan ISWAP suka hallara suna shirin kai wani harin ta'addanci ne ya taimaka wa dakarun, wadanda suka yi amfani da jiragen yakin kasar Nijar suka afka masu da bama bamai da kuma rokoki.
Hakazalika jiragen leken asirin sojojin saman Najeriya da Nijar sun gano ‘yan ta'addan da suka kai wani hari a sansanin sojin Nijer da ke Diffa a daidai lokacin da suke kokarin tsallaka kan iyaka, a nan ma sojojin Artillery sun afka wa jerin gwanon motocin yakin mayakan guda takwas tare da hallakasu baki daya.
Masanin harkokin tsaro Kanar Aminu Isa Kontagora, da ke zama tsohon gwamnan mulkin soji a jihohin kano da Benue, ya ce lallai yanzu lokaci ya yi da za a tunkari ‘yan ta'addan gadan-gadan don kawo karshensu.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum