Tun a washegarin farmakin da shugaban kasar Chadi, Idriss Deby, ya jagoranta kan mayakan Boko Haram a kewayen Tafkin Chadi, rahotanni ke cewa kungiyar ta shiga yunkurin maye guraben mayakan da aka kashe mata.
Yankin Diffa dake daya daga cikin yankunan dake fama da ta’addancin Boko Haram, kungiyoyin ci gaban jama’a na da masaniya a game da faruwar wannan al’amari kamar yadda wani jagoransu Mara Mamadou ya shaidawa Muryar Amurka.
Kasar Chadi ta ce ta kashe a kalla mayakan Boko Haram dubu daya, lamarin da ake ganin ya zowa da kungiyar da bazata saboda haka abin mamaki ne idan har Boko Haram ta bullo da wannan shiri mai kama da matakin huce takaici akan al’umma, a cewar mai sharhi kan sha’anin tsaro Alkassoum Abduourahman.
Matakin kawo karshe ‘yan ta’adda a kasashen yankin Tafkin Chadi, wani abu ne da masana ke nanata cewa ya zama wajibi, amma sai an hada da matakan kyautata rayukan al’umma maimakon dogara ga karfin soji kawai.
Yaki makamancin wanda kasashen tafkin chadi ke kafsawa da ‘yan ta’addan boko haram wani abu ne da masana suka sha nanata cewa wajibi ne a dai bangare a dauki matakan kyautata rayuwar jama’ar yankin dake cikin wannan tashin hankali a maimakon amfani da karfin soja kawai.
Muryar Amurka ta yi yunkurin jin matsayin gwamnatin jamhuriyar Nijar, kan sabon salon da kungiyar Boko Haram ta sa gaba, amma ya ci tura. Sai dai wata majiya na cewa a baya bayan nan hukumomi sun kafa dokar han shiga kewayen Tafkin Chadi, tare da rufe wasu daga cikin kasuwannin yankin Diffa.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Sule Muminu Barma.
Facebook Forum