Wani jami’in ma’aikatar tsaron Amurka ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Kamaru ce ta bukaci Amurka ta tura dakarun, a yunkurin kasa da kasa na shawo kan hare haren da kungiyar mai tsats-tsauran ra’ayin addinin Islama take kaiwa a kasashen yammacin Afrika.
Sojojin dai zasu yi shawagi ne ta sararin samaniya musamman a jihar Arewa Mai Nisa da kuma kan iyakokin kasar Kamaru da kasashen Chadi, da Nijar, da kuma Najeriya, inda kungiyar take tada kayar baya.
Ministan harkokin tsaro na kasar Kamaru Jeseph Biti Asomu, yana shirin karbar bakuncin dakarun dari biyu da goma da gwamnatin Amurka tayi alkawarin turawa.
Ba tun yanzu bane kasar Kamaru ta fara neman dauki daga kasar Amurka da abokan kawancenta. Yanzu dai bisa ga dukan alamu, an fara kama hanyar nasara, kasancewa ana gani wadannan dakarun zasu taimaka wajen dakile hare haren na kungiyar Boko Haram.
Tuni al’ummar kasar Kamaru suka fara bayyana goyon bayan wannan yunkurin, tare da kira ga jama’a musamman wadanda ke zaune a wadannan yankuna, su ba hukumomi cikakken goyon baya domin ganin haka ta cimma ruwa.
Ga cikakken rahoton da wakilinmu Muhammad Garba Awwal ya aiko daga birnin Yaounde na kasar Kamaru.
Your browser doesn’t support HTML5