Bita: Gudummawar Coci Don Gina Demokradiyya Mai Dorewa A Najeriya

An fadakadda da mabiya addinai da su yi amfani da koyarwan littafi mai tsarki wajen kawo sauyi da zai tsabtace siyasa da kauda cin hanci da rashawa a Najeriya.

A wani taron bita da wata kungiya da ba ta gwamnati ba, House of Issachar ta shirya wa mabiya addinin kirista, mai taken gudummawar Coci wajen gina demokradiyya mai dorewa a Najeriya, an faddakar da mahalarta taron kan samar da kyakykyawan ginshiki na nuna adalci ga kowa da kauda cin hanci da rashawa da kuma hana musayan kudi lokacin zabe.

A lokacin da yake gabatar da kasida a wurin taron bitar, Farfesa Dakas Clement Dakas, ya ce addini tafarki ne na yin gaskiya.

Shugaban kungiyar House of Issachar, Barista Yakubu Sale Bawa, ya ce sun shirya taron don zaburar da al’umma aiwatar da hakkin kawo sauyi a sha’anin gudanar da harkokin shugabancin da Allah ya basu don walwalar ‘yan Najeriya.

Saurari cikakken rahoton wakiliyarmu Zainab Babaji daga Jos:

Your browser doesn’t support HTML5

Bita: Gudummawar Coci Don Gina Demokradiyya Mai Dorewa A Najeriya