Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa: Buhari Na Bukatar Kafa Kotunan Musamman


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga majalisar dokokin kasar da ta gaggauta amincewa da kudurin dokar kafa kotunan musammam da za su yi shari’o’in kararrakin da suka danganci cin hanci da rashawa.

Wannan a cewar shugaba Buhari, zai taimaka ainun wajen magance matsalar tsaiko da ake samu a shari’o’in cin hanci da rashawa a kotunan kasar.

Buhari ya yi wannan kiran ne sa’adda ya bude wani taron kasa na kwanaki biyu a kan yaki da cin hanci da rashawa a aikin gwamnatin, wanda hukumar yaki da ayyukan cin hanci da rashawa ta ICPC, tare da ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya suka shirya a fadar gwamnatin da ke Abuja.

Ya ce kafa kotuna na musamman na shari’o’in cin hanci da rashawa, zai baiwa gwamnatin damar cimma burin ta na ganin an kwato dukiyoyi na haram da kadarorin da aka mallaka ba bisa ka’ida ba, da kuma uwa uba, hukunta wadanda aka kama da aikata irin wadannan laifuka.

Shugaban kasar yayi amfani da damar taron inda ya bayyana irin illoli da matsalar cin hanci da rashawa ya ke haifarwa ga tattalin arzikin Najeriya da rayuwar al’ummar ta.

Da ya ke karin haske a kan jawabin shugaban kasa a wurin taron, Kakakin Fadar Shugaban Kasa Garba Shehu, ya ce “akwai damuwa a bangaren gwamnatin da hukumar ICPC, yadda ake daukar tsawon lokaci kafin a yanke hukunci a shari’un da suka shafi cin hanci da rashawa a kotunan yau da kullum".

Garba Shehu ya ce wannan yanayin yana shafar kudurorin gwamnatin na inganta sha’anin ilimi da yaki da ta’addanci da kalubalen tsaro da ya addabi yankuna da dama na kasar.

Ga karin bayani daga Umar Faruk Musa:

Buhari yayi kira da a kafa kotunan musamman na cin hanci da rashawa
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG