Al’ummomin Irigwe da Bace dake karamar hukumar Bassa a jahar Pilato sun yi wata yarjejeniyar zaman lafiya don ci gaban yankunan su.
Al’ummomin sun yarda suyi amfani da sulhu wajen magance matsalar kan iyaka, tsaida ayyukan bata gari dake haddasa kashe-kashen jama’a da lalata dukiyoyinsu, da kuma yaki da yawaitar makamai a yankin.
Shugaban raya al’ummar Irigwe, Sunday Abdu, wanda ya karanta yarjejeniyar a madadin al’ummomin biyu ya bukaci hukumar shata kan iyaka ta kasa da ta sake duba batun kan iyakar al’ummomin biyu.
Ga cikakken rahoton Wakiliyar Muryar Amurka a Jos, Zainab Babaji.
Facebook Forum