Wani mai magana da yawun jam’iyar Labour ta kasar Birtaniya ya fada cewa shugaban jam’iyar Jeremy Corbyn, zai so suyi muhawara gaba da gaba tare da firaminista Theresa May, akan kokarinta na ganin an amince da ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai da kuma makomar kasar gaba daya.
Firaminista Theresa May, ta bada shawara a wata hira da tayi da jaridar 'The Daily Telegraph' tana da sha’awar ta kalubalanci Corbyn, da suyi muhawara a talabijin akan ficewar kasar Birtaniya, daga tarayyar turai yayin da ta kaddamar da kamfe din ta na neman amincewa da yarjejeniyar ta hanyar 'yan majalisar kasar.
Mintoci arba’in kacal ya dauki May da sauran Shugabannin Kungiyar Tarayyar Turai suka saka hannu akan amincewa da yarjejeniyar fitar Birtaniya daga Tarayyar Turai, bayan shekaru biyu da suka shafe suna shawarwari.
Sai dai har yanzu akwai kalubale dake tattare da kokarin samun amincewar masu ruwa da tsaki na Birtaniya game da yarjejeniyar.