Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump Zai Duba Rahoton Binciken Kisan Dan Jarida Kashoggi


Shugaban Amurka Donald Trump zai duba rahotan binciken da gwamnatinsa ta gudanar kan mutuwar dan jaridar Washington Post Jamal Khashoggi.

A yau Talata, ake sa ran Shugaban Amurka Donald Trump, zai duba rahotan binciken da gwamnatinsa ta gudanar, kan mutuwar dan jaridar Washington Post Jamal Khashoggi, wanda aka kashe a karamin offishin jakadancin Saudiyya da ke Santanbul a kasar Turkiyya.

Kafafen dillancin labarai da dama a Amurka, sun ruwaito jami’an tattara bayanan sirri na CIA suna cewa, Yarima Mohammeed Bin Salman ne ya ba da umurnin a kashe dan jaridar a ranar 2 ga watan Oktoba.

Koda yake, a ranar Asabar din da ta gabata, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce har yanzu ba a cimma matsaya ta karshe kan wannan batu ba.

Su dai hukumomin Saudiyya sun musanta cewa Yarima Salman, na da hannu a wannan kisa na Khashoggi, yayin da shi kuma shugaba Trump, ya kwatanta rahotanni da ke danganta Yarima Salma da kisan a matsayin marasa tushe.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG