Wasu mutanen da rikicin ya bi ta kansu, yanzu haka an mayar da su nakasassu. Zanga-zangar da suka fara yi jiya Litinin a fadin kasar Kamaru na zuwa ne, bayan wani fada da ya kaure a karshen mako, wanda yayi sanadiyar rayukan ‘yan bindigar 25 haka kuma an kashe wasu sojoji.
Martin Ndende mai shekaru 54 na daga cikin daruruwan masu dauke da nakasa da suka fito zanga-zanga kusa da ma’aikatar tsaro jiya Litinin.
Ndende, wanda kwashe shekaru 35 yana fama da lalurar rashin ji, ya je yankin masu amfani da ingilishi domin ya koyar da ilimin falsafa, a arewa maso yammacin garin Kom a watan Satumbar shekarar 2017.
Ko wata guda bai kai ba a makarantar, ‘yan bindiga suka kai musu hari suka kone makarantar saboda basu bi umarnin rufe makarantar ba.
Ndende ya ce yana daga cikin mutanen da suka fuskanci ta’addancin ‘yan bindiga a yankin masu amfani da ingilishi na Kamaru. ya ce yaje ne domin ya koyar da yara a yankin, saboda masu kishin kasa na gaskiya da iyaye ba zasu taba yarda da abin da zai kawo cikas ga ilimin yaransu ba. ko da kuwa a kasashen da ake yaki, akwai kariya da ake baiwa yara don su sami damar ci gaba da neman iliminsu.
Facebook Forum