Shugaban Amurka Donald Trump, jiya Lahadi, yayi ikirari ba tare da ya gabatar da wata shaida ba cewa, binciken da ake gudanarwa kan danganatakr kwamitin yaken neman zabensa a 2016 da kasar Rasha, doka bata amince dashi binciken ba.
WASHINGTON D.C. —
A kalaman da ya furta ta Tweeter, shugaban na Amurka, yace binciken da lauya na musamman Robert Mueller yake gudanarwa "haramtacce ne" yace ana ci gaba da binciken ne domin neman laifi da za'a lakaba masa.
Sai dai idan za'a tuna ma'aikatar shari'a ta Amurka ce ta nada shi, kuma alkalai sun yanke hukuncin cewa binciken yana kan ka'ida.
Kamar yadda ya saba, Trump ya musanta cewa akwai hadin baki tsakainin kwamitin yakin neman zabensa da Rasha, yace yace abokiyuar karawarsa Hillary Clinton ce ta hada baki d a Rasha. Ya kwatanta gungun lauyoyi da suke aiki da Mueller a zaman "fusatattun 'yan Democrats 17" da suka dage ka'in da na'in domin nemo laifi. Yace "Babu adalci ko kadan," kuma matakin bai yiwa kasar mu dai dai ba.