Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfani Zai Biya Miliyan 1.5 Sanadiyar Rikicin Hana Ma'aikata Sallah


Wani ladani yana kiran sallah a Masallaci
Wani ladani yana kiran sallah a Masallaci

Ma'aikatan sun yi boren ne na tsawon kwanaki uku, bayan da aka ki kebe masu lokacin zuwa su yi salla.

Wani kamfanin sayar da nama a Amurka ya amince zai biya wasu ma’aikatansa Musulmi dala miliyan 1.5 a matsayin diyya, wadanda ya kora bayan da suka yi yajin aiki.

Ma'aikatan sun yi boren ne na tsawon kwanaki uku, bayan da aka ki kebe masu lokacin zuwa su yi salla.

A jiya Juma’a Hukumar da ke tabbatar da adalci wajen daukan ma’aikata a Amurka, wacce ake kira EEOC a takaice, ta sanar da wannan matsayar da aka cimma tsakanin kamfanin sayar da naman mai suna Cargil Meat Solutions Corporation da wasu ma’aikatansa Musulmi 138.

Aksarin wadannan ma'aikata baki ne ‘yan kasar Somaliya.

Wannan rikici ya faro tun a shekarar 2016, bayan da kamfanin ya kori ma’aikatan a lokacin da suka kauracewa wajen aikin na tsawon kwanaki uku a garin Fort Morgan a jihar Colorado da ke yammacin Amurka saboda an ki ware masu lokacin zuwa su yi salla.

Daga baya, kamfanin ya kuma sauya dokokinsa inda yakan ba da dan takaitaccen hutu, domin barin ma'aikatansa Musulmi su rika zuwa suna sallah.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG