Daya daga cikin mutanen da suka kafa kamfanin Microsoft, Bill Gates, ya hada kai da sauran hamshakan attajirai wajen yaki da cutar Alzheimers da ke haddasa matsalar mantuwa da ke shafar lafiyar kwakwalwa.
Gates tare da Leonard Lauder da iyalan Dolby da Charles da kuma gidauniyar Helen Schwab, za su zuba kudi Dala miliyan 30 a fannin bincike nan da shekaru uku masu zuwa, domin a kirkiro da sabbin hanyoyin da za a iya gane mutum ya kamu da cutar ta mantuwa cikin sauri.
A watan Nuwamban da ya gabata, Gates shi kadai ya kashe Dala Miliyan 50 a wani mataki na yaki da cutar, yunkurin kuma da ya tattaro kamfanoni da gwamnatoci wajen yaki da cutar ta mantuwa da ke shafar lafiyar kwakwalwa.
Nau’in cutar Alzheimers da ke haddasa matsalar mantuwa, na shafar kusan mutum miliyan 50 a duk fadin Duniya.
Masana kimiyya da masu bincike a wannan fanni a makarantu da wasu wuraren neman ilmi a fadin duniya zasu amfana da wadannan kudade, kungiyoyin agaji da kamfanoni dake bincike a wannan fanni suma suna daga cikijn wadanda zasu amfana da wadannan kudade.