A ranar Litinin, majalisar dokokin Masar ta zartas da dokoki, ciki har da daya wadda za ta bai wa 'yan kasashen ketare izinin zama 'yan kasa, muddin suka ajiye kudi dala dubu dari hudu, kimanin Naira miliyan 150 a wani bankin kasar.
Hakan zai dogara ne idan mai ajiyar ya kyale kudaden a bankin na tsawon shekaru biyar, kuma ya ci gaba zama a kasar.
'Yan majalisar sunce wadanda za su ci gajiyar wannan shiri ba za su sami izinin shiga ko 'yancin siyasa ba, sai bayan shekaru biyar.
Wasu 'yan majalisa da masu sukar lamirin a kafofin sada zumunta, sun zargi Shugaban kasar Abdel Fattah al-Sisi da sayar da 'yancin zama dan kasar ga masu zuba jari.
Facebook Forum