Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Donald Trump Yace Bai Yarda Rasha Tayi Shisshigi Ba


Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin
Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin

Manyan kungiyoyin leken asirin Amurka da kasashen tarayyar Turai sun nuna kaduwa da kushe kalaman shugaba Trump, akan hakikance cewa kasa Rasha bata yi wa zaben Amurka katsalanda ba.

Dukannin manyan hukumomin leken asirin Amurka sun hakikance cewa hukumomi a Moscow sun yi katsalandan a zaben, kuma batun ke kan gaba a binciken da ake gudanarwa da ya shafi jami’an Rasha da kuma ma’aikatan ofishin yakin neman zaben Trump

Wakilan majalisar dokokin Amurka daga jam'iyun duka biyu, da kuma jami’an leken asirin Amurka sun kushewa kalaman Trump tun kafin ya kama hanyar komowa gida.

A halin da ake ciki kuma, kasashen Turai sun nuna kaduwa ganin yadda shugaban Amurka Donald Trump yake da sha’awar kulla dangantaka da Rasha da takwaran aikinsa Vladimir Putin, da suka hakikanta cewa, zai zama barazana ga harkokin tsaro.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG