Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Tarayya Amurka Ta Yi Takaicin Kalaman Trump


Shugaba Trump da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin a ganawar da suka yi a birnin Helsinki.
Shugaba Trump da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin a ganawar da suka yi a birnin Helsinki.

Shugaban Amurka Donald Trump tsaye a gefen shugaban Rasha Vladimir Putin, ya ayyana cewa bai ga wani dalili da zai sa ya amince Rasha ta yi shishshigi a zaben Amurka wadda ya kai shi ga zama shugaban kasa. Duk da cewa manyan hukumomin leken asirin Amurka sun hakikance cewa hukumomi a Moscow sun yi hakan.


Wakilan majalisar dokokin Amurka daga jam'iyyun duka biyu sun maida martani kan matsayar na Shugaba Trump tare da nuna kaduwa da takaicin ganin ya gaza goyon bayan hukumomin leken asirin Amurka a taron manema labarai na hadin gwiwa da yayi da Shugaban na Rasha.


"Tilas shugaban na Amurka ya gane cewa Rasha ba kawar mu ba ce," inji kakakin majalisar wakilai Paul Ryan dan Republican, a cikin wata sanarwa da ya bayar.

Tilas Amurka ta dukufa wajen ladabtar da Rasha tare da kawo karshen mummunar hare haren da take yiwa tafarkin demokradiyyarmu." Inji Ryan.


Senata John McCain, wanda dadadden mai sukar Trump ne, ya ce "Taro da manema labarai da aka yi yau a Helsinki, shine mataki mafi zubda mutunci da wani shugaban Amurka ya taba yi da za'a iya tunawa. Barnar da rashin basira da girman kai da nuna kauna ga shugabannin 'yan kama kariya bashi misaltuwa."


Shugaban kwamitin harkokin waje a Majalisar dattijai, Bob Corker ya ce "Kalaman Trump yasa ana yi wa Amurka kallon "kanwar lasa" kuma a cewarsa, hakan yasa "wannan lokaci ya kasance maras dadi ga kasar mu."


Haka suma 'yan jam'iyyar Democrat basu wata kumbiya kumbiya ba a nasu martanin. Shugaban marasa rinjaye Chuck Schumer daga jahar New York, yace "shugaban na Amurka ya goyi bayan matsayar Putin, kan dukkan itifakin da hukumomin leken asirin Amurka suka yi. Ya amince da maganar KGB, maimakon bayanan maza da mata ma'aikatan CIA.


Dan majalisar wakilai daga Virginia dan Demokrat Gerry Connolly ya fada ta shafin Twitter cewa, Trump ya sami sabon aiki: Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Rasha.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG