Matan da aka yiwa wannan aiki dai sun nuna godiyar su da jin dadin su ga yadda suka sami saukin cutar, inda har suka nuna jin dadin yadda ake kula dasu a Asibitin.
Babban likitan da ke kula da masu yoyon fitsari a Asibitin Jan Kwano, Sunday Lengmang, yace idan mace ta haihu tana yoyon fitsari awa 12 zuwa 16 babu damuwa, amma idan har ya wuce awa 16 to zai iya yiwuwa mafitsarar mace ce ta fashe, wanda hakan na iya faruwa alokacin da kan yaron da zata haifa ya danne kan mafitsarar har ya janyo ta fashe.
Shima babban jami’in da ke kula da bangaren masu cutar yoyon fitsari a hukumar raya kasashe masu tasowa ta kasar Amurka wato USAID a Najeriya, Dakta Habib Sadauki, yace ya kamata gwamnatoci su bada himma wajen tallafawa masu cutar.
Asibitin Jan Kwano dai yayi nasarar yin aiki wa mata masu yoyon fitsari fiye da dubu Goma a cikin shekaru Ashirin da Hudu da take gudanar da aikin.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5