ABUJA, NIGERIA - Wannan bukata ce suka nuna suna son a samar wa yara mata a dukkan fannonin rayuwa don samun canji da ci gaba mai dorewa a Najeriya.
Shawarwari, bukatu da kuma korafe-korafen da ke fitowa daga bakin ‘yan makarantan sakandaren gwamnati dama masu zaman kansu a birnin tarayyar Najeriya, Abuja a yayin bukin ranar ‘ya’ya mata ta duniya kenan inda wasu ke neman a basu ababen more rayuwa a makarantunsu wasu kuma ke nuna bukatar a sauya yanayin tunani a kan ababen da mata zasu iya yi.
Taken ranar ta bana dai shi ne “Dada himma kan batun 'yancin 'ya'ya mata”, jagororin jin dadinmu kamar yadda aka wallafa a shafin yanar gizon asusun tallafa wa yara na Majalisar Dinkin Duniya na UNICEF.
Ranar ‘ya’ya mata ta duniyar dai ta samo asali ne a ranar 19 ga watan Disambar shekarar 2011 a babban taron Majalisar Dinkin Duniya inda aka amince da kuduri mai lamba ta 66/170 na ayyana ranar 11 ga watan Oktoba a matsayin ranar yara mata ta duniya, don amincewa da ‘yancin kula da ‘ya’ya matan da kalubale na musamman da suke fuskanta a duniya.
A yayin murnar zagayowar ranar ta shekarar 2022 da kuma cikar shekara 10 da kafa ranar, asusun UNICEF da wasu masu ruwa da tsaki a Najeriya sun bayyana cewa an fara shawo kan wasu matsaloli da suka shafi yara mata a gwamnatance, tare da basu damammaki a cikin kasar da kumą wasu kasashen duniya.
Wasu rahotanni sun yi nuni da cewa, wasu yara mata ‘yan kasa da shekaru 18 sun nuna bajinta a fanonnin rubuta littafi, Kere-keren manhajoji, samun guraben karatu a manyan jami’o’in kasashen Amurka, Igila, Australia da dai sauransu.
Saidai wasu iyaye mata sun ce ya zuwa yanzu akwai jan aiki a gaban dukkan masu ruwa da tsaki, inda malama Bara’atu Nasidi, wacce ta shirya wani taron tafka muhawarra a kan maudu’an da suka shafi rayuwar ‘ya’ya mata a wannan ranar, ta ce kamata yayi gwamnati da saura masu ruwa da tsaki su rika tuna cewa ‘ya’ya mata mutane ne kuma a rika basu damammaki kaman saura takwarorinsu maza.
A nata bangare, kwararriya a fannin sanin halayyar ‘dan Adam da bada shawara ga ma’aurata, ta ce ranar ‘ya’ya mata ta duniya na da mahimmanci saboda ana karfafawa mata gwiwa a kan duk wani buri da suke da shi na rayuwa abu ne mai yiyuwa, muddin ana basu gudunmawa da goyon bayan da suke bukata.
A yayin jawabi a wurin taron tattaunawa a kan ‘ya’ya mata na kasa tare da masu ruwa da tsaki na ranar ta yau, mai dakin shugaban Najeriya, sanata Oluremi Tinubu, ta jadada mahimmancin karfafa su da ilimi ta hanyar zuba jari zai samar da da makoma mai kyau ga kasar.
Manufar amincewa da wannan rana ta duniya da farko dai ita ce ƙara wayar da kan jama'a game da matsalolin da ‘ya'ya mata a duniya ke fama da su, da suka haɗa da rashin samun ilimi, rashin isasshen abinci mai gina jiki, auren dole, tauye musu haƙƙi, da dai sauransu.
Saurari cikakken rahoto daga Halima Abdulrauf: