Ministan kiyon lafiya da jin dadin al'ummar Jamhuriyar ya yi wa yan kasar jawabi a kafofin yada labarai na gwamnati, domin fadakar da su a kan muhimancin wannan ranar ta yau 11 ga watan Yuli.
Docteur Idi Illiasu Mai Nassara, ya yi bayyanin cewa, lalle, duk da kokarin warewa diya mata kaso 25 cikin 100, na mukamai na siyasa a kasar, har yanzu da sauran rina a kaba a fafutukar da kasar ta Nijer ke yi domin samae wa diya mata 'yanci da walwala na kutsawa a dama da su a harakokin duniya musaman a cikin wannan kasar.
Kasar Nijer ta rattaba hannu ga yarjejeniyoyi na duniya da dama da ke kare hakkokin mata da yara a cikin shekaru 20 da suka shude.
Wannan ya ba da damar rage wariya ga mata, tare da damawa da su a harakokin mulki da na yau da kullum a cikin kasar, ko da ya ke akwai sauran wadansu dabi'u da ke kawo cikas ga wannan fafutukar, kamar nuna wariyar wani jinsi, da ma ware mata a harakokin ilmi, mulki da na tattalin arziki.
Jamhuriyar Nijer dai, na kunshe da al'ummar da yawan ta ya kai 26,062,585 a ranar da ya ga watan Yuly 2023.
Yawan al'ummar kasar na karuwa da kashi 3.9 a cikin 100, da ke kasancewa daya da ga wanda ya fi yawaita a duniya ta la'akari da karancin amfani da al'ummar kasar ke yi musamman diya mata da hanyoyi na zamani na ba da tazara tsakanin haihuwa da haihuwa.
A cewar Hawa Meina wata yar Fafutukar kare hakkokin ma'aikata a Nijer, kuma yar gani-kashe nin kare hakkokin malaman makarantar boko yan kontaragi, yanzu an gane kuma an amice cewa, tafiyar nan ba ta yi sai da diya mata.
Hawa Meina ta ci gaba da cewa, sun soma ganin nasara a fannin siyasa, ta la'akari da gogawa da matan ke yi a takarar mukaman siyasa kala-kala da 'ya'ya maza.
Wannan ranar ta tunawa da al'mma a yau, dama ce ta fadakar mutanen duniya inda a ka kwana wajan kyautata rayukan al'ummar duniya.
Saurari rahoton a sauti:
Dandalin Mu Tattauna