Gammayyar kungiyoyin matan dai sun bayyana cewa zaben shekarar 2023 da ake shirin yi a Najeriya zai sha bamban da zabukan baya, domin an dade ana ruwa kasa na shanyewa. Sun ce wannan karon dole ne duk wani dan takarar shugaban kasa ya bayyana manufofinsa da shirye-shiryen da ya tanadar wa mata da yara mata kafin su mara masa baya. Bayan haka sun ce mata na bukatar a basu dama a matakai dabam daban a kasar.
Hajiya Saudat Mahdi, babbar sakatariyar kungiyar kare hakkokin mata ta WRAPA a Najeriya ta yi karin haske, tana mai cewa sun kira ‘yan takarar ne don kara gabatar da bukatunsu, ciki har da neman a basu dama wajen gina kasa da jagorancin Najeriya.
Matan sun kuma koka kan yadda ake mayar da su saniyar ware a harkokin da suka shafi siyasa a kasar, batun da dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar Action Alliance (AA) Manjo Hamza Al’mustapha ya ce jam’iyyarsa ta tsara hanyoyin inganta rayuwar mata a kasar da suka sha bamban da sauran jam’iyyu. Ya kuma ce sun duba wasu kudurori guda 8 da Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gwamnatoci su yi wa mata.
Shi ma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar SPD Adewole Adebayo cewa ya yi jam’iyyarsa a shirye take ta bada goyon baya ga mata dari bisa dari.
“Mu da ke neman shugabancin kasar nan mu na yi ne don al’umma, kuma jam’iyyata ta bambanta da sauran, mu ba irin wadanda ke amfani da mata don daura zani ba ne da yin wake-wake, mun fito ne don wannan dalilin na basu goyon baya dari bisa dari,” a cewar Adebayo.
Cikin jerin sunanyen ‘yan takara na karshe da zasu fafata a zaben shekarar 2023 da hukumar zabe ta INEC ta fitar, mata 374 a cikin ‘yan takara 4,223 ne kacal ke neman kujeru 469 a Majalisar Dokokin kasar; 109 a Majalisar Dattawa sai 360 a Majalisar Wakilai. Lamarin da ke nuna rashin kyawun wakilcin mata a fagen siyasa a kasar da ta fi kowacce yawan jama’a a Afirka, kuma daya daga cikin manyan kasashen da ke bin tsarin dimokradiyya a duniya.
Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim.