Ministan Muhalli Malam Muhammad Mahmud, wanda ya wakilci Shugaba Buhari wajen bikin bada sandar sarautar Zazzau ga Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau na goma sha tara (19), ya nemi sabon sarkin da ya bai wa gwamnati hadin kai.
Ya ce gwamnati na da yakinin cewa Sarkin zai yi amfani da gogewa da sanayyar shi wajen bin salon gwamnati game da dawo da zaman lafiya da kyautata zamantakewar al'uma wadanda su ne ruhin kawo ci gaba.
A karon farko dai tun bayan sanar da zaben Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon Sarkin, gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-rufa'i ya nuna hikimar nadin. Inda ya fadi cewa, wannan bikin mika ragamar sarautar Zazzau ga sarki na sha tara ya na gudana ne shekaru dari chur da gwamnan mulkin mallaka na yankin Arewa ya tube kakan Sarkin na Zazzau Malam Aliyu Dan-sidi ba bisa adalchi ba.
Saboda haka gurbin da aka samu na sarkin Zazzau shi ya bai wa gwamnatin Kaduna daman gyara rashin adalchin mulkin mallaka da kuma komawa kan tsarin da ake amfani da shi wajen nadin sarakuna karkashin daular Usmaniyya ta sokkoto.
Jawabin sabon sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ma ya yi kama da na gwamnan jihar Kaduna saboda ya tuna baya har sai da ya zub da hawaye.