Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

El-rufa'i Ya Bayyana Matsayin Gwamnati Game Da Zaben Sabon Sarkin Zazzau


 Ziyarar Sabon Sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ga gwamna Nasiru El-rufa'i.
Ziyarar Sabon Sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ga gwamna Nasiru El-rufa'i.

A karon farko tun bayan nadin sabon sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-rufa'i ya bayyana matsayin gwamnati game da zaben sabon sarkin.

Da yake jawabi yayin karbar bakuncin sabon Sarkin Zazzau da tawagarsa yayin ziyarar sabon Sarkin ta farko zuwa gidan gwamnatin Kaduna tun bayan nadin shi, gwamna El-rufa'i ya bayyana cewa nadin sabon Sarki wani shiri ne daga Allah.

Gwamnan ya yi kira ga sabon sarkin na Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli da ya hada kawunan gidajen sarautar Zazzau guri guda. Ya bayyana cewa kowanne dan Sarki yana so ya zama Sarki wata rana, amma ana yin sarki guda daya ne kawai a lokaci guda, sabili da haka da yake shi ne Allah ya ba sarauta a wannan lokaci hakin ya rataya a kanshi na hada kawunan al’ummar masarautar da kuma rungumar kowa.

an-nada-alhaji-ahmad-nuhu-bamalli-a-matsayin-sarkin-na-19-na-zazzau

hira-da-mai-martaba-sarkin-zazzau-alhaji-ahmad-bamalli

mahukuntan-jihar-kaduna-sun-musunta-batun-rarraba-masarautar-zazzau

Gwamna El-rufa’I ya ce duka lokacin da aka shiga neman wani abu, akwai wanda zai samu akwai kuma wanda zai rasa, saboda haka abu mafi muhimmanci a wannan lokacin shi ne neman hadin kan al’ummar masarautar da kuma kasa baki daya.

Ziyarar Sabon Sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ga gwamna Nasiru El-rufa'i.
Ziyarar Sabon Sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ga gwamna Nasiru El-rufa'i.

Maganar tunkatar matsalolin da ke addabar jahar Kaduna da kasa baki daya na cikin abubuwan da gwamna Nasuru Ahmed El-rufa'i ya nanatawa sabon sarkin na Zazzau a wannan ziyara da ya kawo. Yace Allah ya ba Basaraken sarauta a wani mawuyacin lokaci da ake fuskantar matsaloli a masarautar, da jihar ta Kaduna da kuma kasa baki daya.

Matsalolin da gwaman Elrufa’I ya ce ana fuskanta sun hada da matsalar rashin aikin yi tsakanin matasa, da matsalar shaye-shaye, da rashin ababan jin dadin rayuwa da suka hada da rashin karatu, da kiwon lafiya da sauran ababan jin dadin rayuwa da zasu taimaka wa matasa. Gwamnan ya ce kasancewa sabon Sarkin ya yi ayyuka a wurare da dama, yana da kwarewa da kuma damar bada gudammuwa domin shawo kan wadannan matsaloli.

Tun bayan sanarda sunan Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau dai ake ta yawo da rade-radin rarrabuwar kawunan gidajen sarautar ta Zazzau amma sabon sarkin ya ce kawunan gidajen duka na hade su ke. Yace al’u mmar masarautar sun karbe su da hannu biyu. Ya kuma yi alkawarin zama uba ga kowa domin ci gaban masarautar da jihar baki daya.

Ziyarar Sabon Sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ga gwamna Nasiru El-rufa'i.
Ziyarar Sabon Sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ga gwamna Nasiru El-rufa'i.

Tuni dai wadanda su ka nemi wannan sarauta ta Zazzau su ka yi mubaya'a ga sabon sarkin na Zazzau banda daya daga ciki wanda ke kalubalantar nadin da ya nuna ba a bi ka'ida ba.

Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara cikin sauti.

El-rufa'i Ya Bayyana Matsayin Gwamnati Game Da Zaben Sabon Sarkin Zazzau-3:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG