Yayinda al'ummar Musulmi ke shirye shiryen bikin Sallah karama, hukumar bada agjin gaggawa ta NEMA tana kokarin ganin, suma yan gudun hijira ba'a mance da su ba.
Kamar sauran jama'a, 'yan gudu hijira wadanda suke zaune a sansanonin yan gudun hijira a sakamakon hare haren 'yan Boko Haram, suma suna shirye shiryen yin bikin Sallah.
Wata yarinya mai suna Fadila Mohammed wadda take zaune a irin wadannan sansanin ta fadawa wakilin sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz cewa, da so samu ne, sun fi son su yi Sallah a garuruwansu.
To amma hukumar NEMA tana shire shiryen ganin suma 'yan gudun hijira sun ci moriyar Sallah kamar sauran jama'a.
Jami'in dake kula da sansanonin yan gudun hijira a jihar Adamawa, Alhaji Sa'adu Bello yace hukumar NEMA ta yi tanadin kayayyakin abinci dana Salla wa yan gudun hijira , musamman yara.
Your browser doesn’t support HTML5