Biden Zai Kai Ziyara Jamus Da Afirka

Shugaba Biden

A makon da ya gabata aka sauya jadawalin ziyarce-ziyarcen shugaban na Amurka saboda guguwar Milton da ta afkawa jihar Florida

Shugaban Amurka Joe Biden zai tafi kasar Jamus a ranar Alhamis kuma zai ziyarci Angola a makon farko na watan Disamba a cewar fadar gwamnati ta White House.

A makon da ya gabata aka sauya jadawalin wannan ziyarce-ziyarce saboda guguwar Milton da ta afkawa jihar Florida.

Fadar White House ta tabbatar da cewa Biden zai tashi zuwa Berlin don wannan takaitacciyar ziyara a ranar Alhamis.

Wannan zai ba shi dama ya tattauna tare da babban abokinsa, Shugaban Gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, kan goyon bayan kasashensu ga Ukraine a yakin da take yi da Rasha, yayin da rikicin ya shiga wani muhimmin lokaci.

Shirin farko na tafiyar da aka dage ya hada da taro kan yakin da ake yi a Ukraine tare da kasashen kawance a wani sansanin sojin Amurka da ke kasar Jamus.