Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biden, Harris Sun Kai Ziyara Yankunan Da Guguwar Helene Ta Yi Barna


Yayin da Biden yake ziyara a jihar North Carolina
Yayin da Biden yake ziyara a jihar North Carolina

Shugaba Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris sun yi balaguro a ranar Laraba, inda suka kai ziyara yankunan kudu maso gabashin Amurka, don gane wa idanunsu irin baranar da guguwar Helene ta yi.

Marine One, with President Joe Biden on board, flies over Lake Lure and around areas affected by Hurricane Helene near Chimney Rock, N.C., Oct. 2, 2024.
Marine One, with President Joe Biden on board, flies over Lake Lure and around areas affected by Hurricane Helene near Chimney Rock, N.C., Oct. 2, 2024.

Yayin da Biden ya kai ziyara North Carolina da South Carolina, ita Harris kuma ta tafi Augusta a Georgia.

“Sai an kashe biloyoyin dala za a shawo kan guguwar, da duk al’ummomin da balai’n ya rutsa da su, abinda Biden ya fada Kenan bayan da ya kewaya yankin North Carolina da guguwar Helene ta ratsa cikin jirgi mai saukar ungulu. “Ga shi kana gani karara yadda iskar ta dauke gidaje daga wani bangaren har ta tsallaka kogi zuwa daya bangaren.”

Ita kuma Harris ta kai ziyara unguwar Meadowbrook tare da Mayor Garnett Johnson da sauran jami’an yankin. Ta ce tana so ta ganewa idanunta irin barnar da ta yi, wannan wani abu ne da basaban ba.

Ta kuma kai ziyara cibiyar Red Cross sannan an yi mata bayani akan irin halin da yankin yake fuskanta.

U.S. President Biden boards Air Force One en route to North and South Carolina, at Joint Base Andrews
U.S. President Biden boards Air Force One en route to North and South Carolina, at Joint Base Andrews

“Mutane suna cikin alhinin sosai da kuma damuwa a sanadiyar wannan guguwar hurricane din, sannan da abubuwan da suka biyo bayan guguwar” inji Harris, ‘wace jam’iyyar Democratsta tsayar a matsayin ‘yar takarar ta. “Muna nan har zuwa karshe.”

Tun farko a ranar Laraba a Washington, Biden ya bada umarni a aike dakarun sojin Amurka su dubu daya (1,000) domin su bada agaji da kuma aikin gano mutane a cikin al’ummomin da guguwar ta Hurricane Helene ta shafa.

Fadar ta White House ta fada a cikin wata sanarwa cewa sojojin zasu “tallafa a bangaren rarrabawa mutane abinci da sauran aiyuka masu mahimmanci.”

Aike dakarun zai kuma taimaka a samu karin ma’aikata da zasu iya zurga zurga, wanda zai baiwa FEMA da sauran hukumomi da suke da alaka da ita su samu damar isa wuraren da lamarin ya fi Kamari cikin dan kankanin lokaci.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG