Biden Ya Baiwa Ukraine Damar YiN Amfani Da Makaman Amurka Wajen Kai Hari Cikin Rasha

Shugaban Amurka Joe Biden da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky lokacin wata haduwarsu a Oval Office na fadar White House a Washington, D. C.

Gwamnatin Biden ta sahalewa Ukraine yin amfani da makaman da aka kera a Amurka wajen kai hare-hare cikin Rasha, kamar yadda wasu jami’an Amurka 2 da wata majiya dake da masaniya game da shawarar suka bayyana a jiya Lahadi

Hakan na zuwa ne a wani gagarumin sauyin ra’ayi game da manufofin mahukuntan birnin Washington akan rikicin na Ukraine da Rasha.

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky

Kasar Ukraine na shirin kaddamar da hare-hare da makamai masu cin dogon zango a kwanaki masu zuwa, a cewar majiyoyin, saidai basu yi karin haske akai ba saboda dalilai na tsaro.

Hakan na zuwa watanni 2 kafin a rantsar da zabebben Shugaban Kasa Donald Trump a ranar 20 ga watan Janairu mai kamawa kuma ya biyo bayan rokon da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya jima yana yi akan a sahalewa dakarun kasarsa yin amfani da makaman Amurka wajen kaiwa sansanonin sojan Rasha dake nesa da kan iyaka.

Sauyin ra’ayin na zuwa ne a matsayin martani ga tura dakarun Koriya ta Arewa da Rasha tayi zuwa filin daga domin karfafa rundunoninta, al’amarin daya tada hankulan mahuntan biranen Washington da Kyiv, kamar yadda wani jami’in gwamnatin Amurka da kuma wata majiya dake da masaniya game da batun suka bayyana.

A jawabin da ya saba gabatar da maraice, Zalensky yace makaman masu linzami zasu “bayyana nasu ra’ayin.”

-Reuters