Bene Mai Hawa 2 Ya Rushe A Yankin Orile Iganmu Na Jihar Legas

Bene mai hawa biyu ya ruguje a Legas

Bene ya ruguje ne da safiyar yau Litinin a yayin da mutane ke shirye-shiryen fara gudanar da harkokinsu.

Wani bene mai hawa 2 ya ruguje a kan titin Amusu, dake shiyar Orile Iganmu ta jihar Legas.

Bene ya ruguje ne da safiyar yau Litinin a yayin da mutane ke shirye-shiryen fara gudanar da harkokinsu.

Wani mamallakin jaridar intanet, Samuel Olatunji, ya wallafa bidiyon ginin lokacin da yake rushewa, a shafinsa na Instagram.

Ba a iya tantance adadin mutanen dake cikin ginin lokcin da ya rushe ba.

Sai dai, sanarwar da tawagar daukin gaggawa ta hukumar agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA) ta fitar tace, rushewar ginin bai rutsa da kowa ba.