Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Na Zargin Rusau Da Gwamnatin Sakkwato Ke Yi Ya Fi Shafar 'Yan PDP


Kasuwar Sokoto
Kasuwar Sokoto

Duk da bugun kirji da tinkaho da wasu gwamnoni a Najeriya ke yi cewa su na gudanar da ayyukan raya kasa, a dayan bangare akwai wasu ayyuka da suke yi wadanda ke sa wasu jama'a kuka saboda asarar da su ke tafkawa.

Jihohin Kano da Sakkwato sun gudanar da ayyukan rusa manyan-manyan gine-gine mallakar wasu mutane, wasu da nufin za a yi aiki a wurin wasu kuma ba wani bayani kuma babu biyan diyya.

Gwamnatin Sakkwato na ci gaba da gudanar da rusau na manya-manyan gine-gine a wurare daban-daban cikin birnin Sakkwato wadanda wasu mutane ne ke da su kuma suna aiki akan su.

Alal misali an rusa wani katafaren ginin rukunin shaguna kan titin zagayen yammacin Sakkwato mallakar wani dan kasuwa Murtala Bawan Allah Mainiyo, wanda mai filin ya ce rigima ce yake yi da wani dan siyasa ya ja aka rusa ginin.

Hakama an rusa wani gini akan titin Zagga mallakar tsohon babban sakatare Aminu Magaji kuma ya ce halacce ya mallaki wannan wuri amma aka rusa shi.

Har iyau an rusa wasu gine-ginen binaye wadanda aka yi shaguna a kan titin Ali Akilu da wani gini kan titin unguwar rogo.

Sai dai kwamishinan filaye, gidaje, safiyo da tsara birni, Barrister Nasiru Aliyu Dantsoho ya ce duk inda aka rusa ginin ya saba ka'ida kuma gwamnati ta nuna alamar a dakatar da aikin aka ki dakatarwa shi ne dalilin da ya sa aka rusa gine-ginen.

Ya ce wasu daga cikin filaye mallakar wasu ne aka kwace aka baiwa wasu a lokacin gwamnatin da ta gabata, wasu kuma ginin da ake yi wurin ne bai dace ba.

Acewar Kwamishinan duk ginin da aka rushe ba bisa ka'ida ba za a biya diyyarsa ba.

Acewar wasu da abin ya shafa kashi tasa'in da tara na gine-gine da aka rusa mallakar 'yan jam'iyar PDP ne mai adawa a Sakkwato shi ya ake yi musu bi-ta-da-kulli.

Kuma sun ce wannan lamarin ya kamata ya zama darasi ga masu mulki yanzu da wandanda suka wuce har ma da masu zuwa nan gaba.

Wannan lamarin a cewar su kokari ne ake yi na dagula ci gaban jiha da talauta mutane da kara tabarbarewar harkokin kasuwanci da ayyukan yi ga jama'a.

Ga rahoton Muhammad Nasir cikin sauti:

Da Alamar Aikin Rusau Da Gwamnatin Sokoto Ke Yi Na Auna 'Yan PDP.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:21 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG