Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rugujewar Wani Gini A Legas Ya Hallaka Ma’aikata 5


Gini da ya ruguje a Legas
Gini da ya ruguje a Legas

Ma’aikata 5 sun mutu lokacin da wani ginin da ba’a kammala ba ya ruguje akan titin Wilson Mba, a rukunin gidaje na Arowojobe, dake unguwar Maryland, ta jihar Legas da safiyar yau Alhamis.

Ginin wanda ake kan ginawa ya ruguje ne da misalin karfe 3 da mintuna 49 na asubahin yau Alhamis a unguwar Maryland dake Legas a tarayyar Najeriya.

Shugaban Hukumar Bada Agajin Gaggawa na jihar Legas (LASEMA), Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa.

Jami’an bada agaji sun bayyana cewa an kubutar da mutane 5, dukkaninsu maza, da ransu daga karkashin ginin daya rushe.

A cewar sanarwar, “nan take aka fara aikin nema da ceton wadanda hatsarin ya rutsa dasu. An zakulo gawawwakin maza 5 sannan aka ceto wasu mazan 4 da ransu, haka kuma jami’an LASEMA dana hukumar kashe gobara ta jihar legas sun ceto wani namijin daya makale a karkashin baraguzan ginin da ransa.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG