Wannan na zuwa ne bayan makonni 2 da Jamhuriyar Nijar ta fara mayar da ‘yan gudun hijirar ta zuwa garuruwansu na asali.
Gwamna Babagana Umara Zulum da shugabanin al’umar jihar ta Diffa ne suka tarbi Shugaba Bazoum a lokacin da ya isa sauka filin jirgin yankin.
Batun tsaro da ayyukan mayar da dubun dubatar ‘yan gudun hijirar cikin gida da na Najeriya zuwa garuruwan da suka fito na kan gaban abubuwan da aka tattauna a yayin wannan haduwa.
Bayan da ya isa masauki Mohamed Bazoum da ke samun rakiyar ministan cikin gida da na tsaron kasa da babban kwamandan rundunar mayakan Nijar ya ziyarci barikin sojan Zone de defense No 5 don karfafawa dakarun tsaro kwarin gwiwa.
"Mun yi fama da tuntube a can baya mun yi rashi amma kuma mun tashi tsaye da kafafunmu yau da gobe ta san kun kara gogewa. Kokarin da kuke bayarwa a ‘yan watanin nan ya matukar yi tasiri sosai wajen samun nasarori sakamakon jajircewar da kwarewarku.
"Saboda haka ne na zo ne in jinijna maku in kuma ce maku muna kan hanyar samun galaba saboda kun gwada ku mazajen daga ne. ko a shekaranjiyan nan kun gwadawa abokan gaba cewa ruwa ba sa’an kwando ba ne kun fatattake su sosai. A yau da safen nan al’umar Diffa ta ba mu tabbacin gamsuwa da ayyukan da kuke yi". In ji Bzaoum.
A ci gaba da wannan rangadi Shugaban kasa ya jagoranci taron kwamitin tsaro na kasa conseil national de securite a yammacin Alhamis inda ya zarce da tattaunawa da shugabanin al’umar Diffa akan makomar ‘yan gudun hijira tare da batun farfado da aiyukan noma kiwo da kamun kifi.
A ranar Juma'a ake sa ran tawagogin Bazoum da Zulum z asu bakunci garin Baroua inda rukunin farko na ‘yan gudun hijira sama da 5000 ya koma gida a tsakiyar watan jiya.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5